Hotuna: Yadda Tinubu Ya Yi Buɗa-baki Da ‘Yan Majalisa
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi baƙuncin ‘yan majalisar wakilai a daren Litinin yayin liyafar buɗa-baki.
A jawabinsa, ya jaddada cewa shugabanni dole ne su yi mulki da tausayi da adalci.
A yayin taron, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya jagoranci bayar da gudunmawar naira miliyan 705 daga albashin ‘yan majalisar domin tallafa wa ayyukan jin-ƙai a Nijeriya.
0 Comments