Ƴan majalisar wakilai sun yi wa talakawan Nijeriya abin a yaba
A Yammacin ranar Litinin din nan, bayan tawagar jiga-jigan majalisar wakilan Najeriya sun yi buda baki da Tinubu, sun dakko cak din zunzurutun kudi har Naira miliyan ɗari bakwai da biyar, suka mika wa Tinubu suka ce ya taimaki talakawa da su.
Sun bayyana cewa sun daɗe suna ta ƙuhurtun tara waɗannan kudaden, inda suke ware kaso 50% daga cikin albashinsu na watan July 2024 har zuwa December 2024, don kawai su ga sun tara kudaden sun kyautata rayuwar talakawa da su
0 Comments