Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Hon. Albani ya sauke nauyin


Hon Albani ya sauke nauyin

Daga Idris Umar Zariya 

A yau ne shugaban karamar hukumar Sabon Gari kuma shugaban kungiyar ciyamomin na jihar Kaduna Honorabul Abubakar Jamilu Albani Samaru ya sauke nauyin da gwamna Uba Sani ya bashi na tallafin azumi ga shuwagabannin jamɓiyar APC na ƙaramar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Taron an gudanar dashine a bubban ɗakin taro na aikin Hajji dake harabar sakatariyar ƙaramar hukumar Sabon Gari.

Wakilinmu ya hango iyaye da shuwagabannin jambiyun APC na ƙaramar hukumar ta Sabon Gari maza da mata na sauraren manyan manyan jawabai na kare duk wani barazana da zai iya taɓa jama'ar karamar hukuma Sabon Gari baki ɗaya.

Bayan da shi Honorabul Jamilu Abubakar Albani ya kammala jawabi ya baiwa wasu daga cikin iyaye a wajan damar yin magana akan taron

Honorabul Ali Mancasta na É—aya daga cikin waÉ—anda suka sanya albarka a wajan taron shima fatan Alheri yayiwa Gwamna Uba Sani bisa kyawawan manufofinta na alheri .

Karshe Honorabul Albani  yayi dogon jawabi akan yadda Sanata Uba Sani ya gudanar da wasu muhimman aiyuka a É“angarori da dama.

Shugaban yace, duk nasarorin da jamÉ“iyar APC ke samu a jihar Kaduna na dawowar wasu  manyan mutane jamÉ“iya ta APC  yana daga cikin kokarin da Sanata Uba Sani ke gudanarwa.

Bisa haka ne shugaban yayi kira ga jama'ar karamar hukumar Sabon garin da suci gaba da baiwa Sanata Uba Sani goyon baya don cigaban jihar Kaduna da Nijeriya baki daya.

Karshe ya miƙa Naira milin 10 da manyan buhunan Shinkafa ga ya'yan jamɓiyar ta APC na ƙaramar hukumar Sabon Gari don yin Kasafi kamar yadda gwamna ya bayar da dama.

Kuma yayi kira ga shugabannin mazaɓu da subi tsarin da aka basu na miƙawa kowa hakinshi ba tare da an dannewa kowa hakinsaba.

Daga cikin manyan mutanen da suka sami zuwa wajan taron akwai mataimakin shugaban karamar hukumar Sabon Gari Honorable Kamilu Abdul-Kareem da Garkuwar matasan Alhaji Shamsuddin da Kogunan Safana Alhaji Abubakar Sadiq.

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Post a Comment

0 Comments