Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya raba kayayyakin abinci ga mabuƙata kamar yadda ya saba


Kamar yadda ya saba a duk shekara a lokacin gabatowar watan azumin Ramadana, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky na raba kayayyakin abinci ga mabukata, a bana ma ya yi rabon abincin a Zariya da ma wasu garuruwa. A inda za a ci gaba da wannan rabo har ya zuwa fara azumin Ramadan na bana.

Rabon kayan abincin na yau Talata 26 ga watan Sha’aban 1446 daidai da 25 ga watan Fabarairun din 2025 an soma gudanar da shi ne da misalin ƙarfe 9 na safe. Kayayyakin abincin da aka raba sun haɗa da; gero, masara, shinkafa da sauran su.

Shaikh Badamasi Yaqoub, ɗan uwa ga Shaikh Zakzaky shi ne wanda ya jagoranci wani bangare na raba kayayyakin abincin.

A yayin rabon kayayyakin abincin, Shaikh Badamasi ya shaidawa manema labarai cewa; Shaikh Zakzaky ya jima yana wannan rabon kayayyakin abincin domin tallafawa mabukata. Ya kara da cewa; ko bayan waki’ar Buhari ta Disambar 2015, Shaikh Zakzaky ya ci gaba da rabawa al’umma wannan tallafin.

Kazakila, ya tabbatarwa da manema labarai cewa; ko a halin yanzu Shaikh Zakzaky yana Lebanon wajen jana’izar shugaban Hizbullah, Sayyid Hassan Nasrallah da kuma Hashim Safiyuddin, amma haka nan ya bada umurni ya ce a yi rabon kayan abincin saboda damuwarsa ga al’umma.

“Malam Ibraheem Al-Zakzaky ya saba da wannan rabon kayayyakin abincin tun kafin waki’ar Buhari. Wani abin mamaki shi ne lokacin da aka yi waki’ar Buhari an hallakar masa da komai - gida da dukiya da komai, amma ya ce duk wanda ya saba ba su taimako na azumi ka da a daina a ci gaba da ba su”, ya jaddada.

Ya ci gaba da cewa; “waki’ar ta dauki tsawon shekaru kuma ana ci gaba da bayarwa. Ga shi yanzu Allah ya kawo mu ya fito ga shi kuma an ci gaba da bayar da wannan tallafin.”

Ya tabbatar da cewa mafi akasarin abincin da ake rabawa ba almajiransa bane ke amfana, inda ya ce; “kusan duka kayan abincin nan mutanen gari ake rabawa. Za ku ga harda waɗanda ba ma sunayensu suna yi mana tururuwa a gida, kuma haka nan akan san yadda ake yi suma a ba su na su kason”, in ji shi.

Shehin Malamin ya tabbatar da cewa Shaikh Zakzaky ya kwashe fiye da shekaru 20 yana raba kayan abincin ga mabuƙata a lokacin azumin watan Ramadana. Kuma rabon kayan abincin ana faɗaɗawa zuwa wasu garuruwan dake faɗin kasar nan.

Waɗanda suka amfana da wannan kayan abinci, sun bayyanawa manema labarai farin cikinsu. Tare da addu’a ga Shehin Malamin.

Da yawan waɗanda suka amfana da tallafin abincin sun fito ne daga sassa daban-daban na garin Zariya da kewaye; wanda ya haɗa da cikin garin Zariya, Sabon Gari, Samaru, Bomo, Likoro da sauran su.

Post a Comment

0 Comments