Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Shugaban ƙaramar hukumar sabon Gari da matarsa sun karbi bakuncin matan ciyamomi 23


Shugaban ƙaramar hukumar sabon Gari da matarsa sun karbi bakuncin matan ciyamomi 23

Daga Idris Umar, Zariya

 Honorabul AbubakarJamilu Albani,Samasu da matarsa Hajiya Husaina Nayaya sun karɓi bakuncin matan ciyamomi ƙananan hukumomi 23 dake faɗin jihar Kaduna a cikin wannan satin.

Taron ya gudanane a bubban ɗakin taro dake harabar sakatariyar ƙaramar hukumar ta sabon Gari dake Dogarawa.

Shugaban ƙaramar hukumar ne da kakakin majalisar da matar shugaban ne suka ja ragamar wannan taro.

Bayan buɗe taron da addu'a ne wata kwarariya a fanin lafiya mai suna Dakta Hadiza Marcus daga bubban asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello Zariya wato ABUTH ta gabatar da muƙala akan ciwon lafiya inda ta ja kunnen iyaye mata akan lura da lafiyar ƙanan yara  lokacin haihuwarsu 

Kuma ta nuna masu yadda zasu kula da kansu a bangaren jego.

Dakta Marcus ta bayar da shawara kan muhimmancin kare kai daga zazzaɓin cizon sauro ta kuma karkace da nuna muhimmanci tsafta ga rayuwa dan adam musamman mace.
An gudanar da tambayoyi ga ita Daktan akan abin da ya shafi kiwon lafiyar.

Bayan nan shugaban yayi tsokaci  tare da jan hankali ga gwamnatin kananan hukumomi a kan yadda za a magance matsalolin da ake samu a wajan bayar da tallafi ga jama'a don inganta harkar dogaro da kai.

Shugaban yace, sau da yawa za kaga ana koyawa mutane abinda bai dace da su ba wanda hakan na sanya gwamnatin na yin hasara a wasu lokutan.

Cikin misalin daya bayar yace, sai kaga an baiwa manomi Injin markaɗe maimakon a bashi Injin ban ruwa.

Daga cikin  wanda suka tofa albarkacin bakinsu bayan kammala taron akwai Hajiya Mariya Musa Hamza Uwar Gidan shugaban karamar hukumar Kudan itama godiya tayi tare da jinjina ga shugaban ciyamomin na jihar Kaduna bisa yadda ya karramasu tare da yin masa fatan alheri shi da matarsa da sauran shugabannin ƙananan hukumomi baki ɗaya.

Yayin da uwargidansa take jawabi godiya tare da rufe taron Hajiya Husaina Abubakar Jamilu Albani tace,tayi farin ciki da Allah ya haɗa fuskokinsu a wannan lokaci bisa haka tayi godiya a madadin mijinta da jama'ar ƙaramar hukumar sabon Gari baki ɗaya tace, Allah ya kai kowa gidansa lafiya.
Daga cikin mutanen da suka rufawa taron baya akwai Hajiya Amina Muhammd (Admin and planning) sai Hajiya Nafisa Mustapha dukkansu sun yiwa taron  da mahalarta taron da shugaban ƙaramar hukumar sabon Gari Honorable Abubakar Jamilu Albani shugaban ciyamomi jihar Kaduna fatan alheri

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Post a Comment

0 Comments