Matasan Harkar Musulunci Sun ba da gudummawar Jini Leda 20 ga Al'amma.
A Yau Litinin 20 ga Rajab 1446h 20/1/2025 Dandalin Matasan Harkar musulunci karkashin Jagorancin Shaikh Ibrahim Zakzaky(H) na Da'irar Kano suka bayar da gudummowar Jini Leda 20 ga Marasa lafiya a Asibitin koyarwa na Malam Aminu kano.
Matasan sun Fara bada jinin ne da Misalin karfe shadaya na safe a sahin gwagwaje na Aishatu Abubakar 'HAEMATOLOGY WERD' dake Asitin koyarwa na Malam Aminu Kano.
Matasa 28 'brothers' da 'Sisters' ne sukaje bada gudunmawar Jinin. A lokacin da ake daukar jinin an samu wasu daga cikin 'Yan uwan wasu marasa lafiyan sunzo Neman jinin da za a sawa yan uwansu ciki har da wanda yazo nemawa Mahafiyarsa da take fama da ciwon Sikila Taimakon jinin wacce yake kawota Asibitin lokaci bayan lokaci.
Ma'aikatan dake bangaren na gwajegwajen Jini sun nunu farin cikin su da wannan gagarumar gudunmawa da Matasan suka bada. A baya nan su sun nuna Rabon dasu samu wasu mutane sun zo bada gudummowar Jini sadaka ga marasa lafiya Anfi shekara Daya, Sunyi Godiya ga Yan uwa tare dayin Addu'a ga Jagoran Harka Islamiyya Sheikh Ibrahim Zakzaky(H) wanda bisa Nuninsa ne matasan suke wadannan Ayyukan na taimakon Al'umma A karshe Anyi hotuna tare da Ma'aikatan Asibitin.
0 Comments