Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Makarantar Islamiyya ta Hidayatul Sufyan da ke garin Bassawa ta yaye daluban 31


Makarantar Islamiyya ta Hidayatul Sufyan da ke garin Bassawa ta yaye daluban 31

Daga Fatima Idris 

A ranar Lahadi, 26 ga watan Janairun 2025, ne makarantar Islamiyya ta Hidayatul Sufyan da ke garin Bassawa a karamar hukumar Sabon Gari ta gudanar da bikin saukar karatu tare da haddar Al-Kur'ani da daluban makarantar 31 suka yi.

Wakiliyarmu na daya daga cikin manema labaru da ta halarci taron, ta kuma bayyana mana cewa a cikin daluban, 25 sune suka yi sauka, 6 suka haddace inda daluban suka kasance 13 mata ne yayin da maza kuma su 18. 

Taron ya samu halartar jama'a da dama da suka hada da shugaban karamar hukumar Sabon Gari, Honorable Abubakar Jamilu Albani, iyaye da 'yan uwan dalubai, dalubai, malamai, shehunnai da sauran shugabannin al'umma.

Salihu Ahmad Yahaya shine mai kula da shugaban makarantar, kuma ya yi tarihin makarantar a takaice inda ya bayyana cewa an kafa makarantar ne da malamai 2 a ranar Litinin 11/2/1982 inda ta fara da dalubai 47 maza da mata, ya zuwa yau shekaru 43 kenan kuma ta yaye dalubai sama da 600.

Da ya ke bayanin kalubalen da makarantar ke fuskanta ga wakiliyarmu, shugaban makarantar ya bayyana cewa, "Kalubalen da muke fuskanta na farko dai iyayen yara ba sa son biyan kudin makaranta, kalubalen mu na biyu shine yara ba sa son zuwa makaranta musamman yara maza, to wannan shine babban kalubalen da muke fuskanta." Malam Salihu ya yi kira ga iyayen yara inda ya ce, "Ina kira ga iyayen yara su kula da yaransu, malamai da suke kula masu da yara su malamai suna taimaka masu ne sune wajibi su kula da hakkokin 'ya 'yansu da Allah Ya ba su, dole ne su kula da shi, idan ba su kula da shi ba su Allah zai tambaya a kan haka, ina kira garesu su kula da wannan nauyi da Allah Ya dora masu su hada kai da malamai wajen biyan kudin makaranta da zuwan su da kula tsaftar su da kula da kayan koyo da koyarwa, duk wannan in ba shi to karatu ba zai tabbata ba." 

Ta bangaren nasarorin da makarantar ta samu, Malam Salihu ya bayyana cewa sun samu nasarori daban-daban domin a lokacin da aka kafa makarantar akwai sashe daya ne amma yanzu akwai sashe hudu ne; akwai Islamiyya da aka bude ta matan aure, akwai bangaren hadda, akwai Junior da Senior Secondary da suka bude. Shugaban ya kara da nuni kan muhimmancin ilimi ga su daluban da al'umma baki daya tare da yin kira ga dalubai da su jajirce su yi karatun da zai amfanesu a duniya da lahira, inda daga karshe ya yi godiya.

Munir Aliyu dalubi ne wanda ya haddace Al-kur'ani, kira ya yi da cewa, "Ina kira ga sauran mutane wadanda ba su haddace Al-kur'ani ba da su yi kokari su haddace Al-kur'ani saboda falalarshi da yadda ta ke natsar da mutane." Munir ya bayyana Al-kur'ani a matsayin constitution na duka duniya inda ya yi kira ga dalubai da su kara jajircewa wajen karatu da kuma iyaye wajen biyan kudin makaranta domin yawanci a cewarsa shi ke sa daluban ba sa samun kammalawa sai kuma ya yi godiya da fatan alkhairi ga malamansa.

Halimatu Salihu Ahmad daya daga cikin dulubai ce wadda aka yaye, ita ma kira ta yi ga dalubai da cewa su kara jajircewa da karatunsu domin ta san karatu akwai wahala amma kuma akwai dadi, sai ta kara da cewa, "Ina fata Allah Ya kara daukaka mana makarantarmu da iyayenmu da kuma malamanmu, ina alfahari da iyayena da kuma malamai na." Halimatu ta yi godiya ga mahaifanta domin jajircewarsu wajen ganin ta samu ilimi sai kuma ta yi fatan alkhairi ga al'umma wadanda ba su samu damar da ta samu ba 'ya 'yansu su samu.

An yi taro lafiya an tashi lafiya.

Post a Comment

0 Comments