A ranar Litinin 20 ga watan Janairun 2025 aka gudanar da jana'izar Auwal Yusuf Sambo Rigachikun, babban ɗan Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun.
Jana'izar ta gudana ne a ƙofar gidan Mahaifinsa dake Rigachikun Kaduna.
Shaikh Dr. Ahmad Mahmud Gumi ne ya jagoranci jana'izar.
Marigayin ya rasu ya bar mata uku da ƴaƴa shida.
Jana'izar ta samu halartar ɗimbin al'umma.
0 Comments