Da ace ni Namiji ne, ba zan ce ina son ƴar mutane ba, har sai na san wace ce Mahaifiyarta, don ba zan tsuguna a gaban Uban yarinya domin yin complain ya ce sai dai nayi hakuri shi ma hakuri yake da ta gidan.
Sannan ko da wasa ba zan je neman aure a gidan da power mace ya rinjayi na namijin ba, domin ba lallai na ga dai-dai ba, saboda sawun da na gaba ya taka shi na baya zai taka. Kuma sanin kanmu ne mata a mafi yawan lokaci sun fi maza kwafsawa, sai yasa ma Allah yace maza ne a saman mata. Kuma kai Yallaboi kai daga jin ance maka gidan nan power mace ne yafi, kai kasan da damuwa, domin ba mijin ba ne ya karramata ya bata Award akan power ta yafi nasa. Wanda ko Allah bai ce haka ba, daga jin haka kasan ita ta samarwa kanta ta hanyar da bai da ce ba, domin idan dacewa ce, kai ai kasan ba ayi haka ba.
Zan bar musu kayansu. Don a shari'ance ma haramun ne ka auri uwa kuma ka auri ƴarta. Eh mana, kana aurar yarinya kana ginata akan tsari, daga waje ana rushe maka.
Ra'ayin ƴar jarida Aisha Kazimiyyah
Mene ra'ayinku?
0 Comments