Ministan Jin kai Ya Bayyana Shirin Gwamnatin Tarayya Na Fitar Da ‘Yan Nijeriya Daga Kangin Talauci
Ministan jinkai da rage radadin talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana shirin fitar da ‘yan Najeriya miliyan daya da rabi daga kangin talauci a duk shekara.
Farfesa Yilwatda ya bayyana hakan ne a Kano yayin taron shekara-shekara karo na uku na daraktoci 36 da kula da walwalar jama’a da ci gaban al’umma daga sassan jihar.
Ministan wanda ya samu wakilcin daraktan kula da jin dadin jama’a na ma’aikatar, Peter Adanu-Audu, ya ce a karkashin sabuwar ajandar shugaban kasa Bola Tinubu, ma’aikatar ta tsara babban burin da za a cimma, ta hanyar hangen nesa da kuma kokarin hadin gwiwa tare da dukkan masu ruwa da tsaki.
Don haka ya umurci daraktocin da su himmatu wajen kawar da kalubalen da ke kawo cikas ga shirye-shiryen ci gaban al'umma tare da samar da hanyoyin isar da ayyukan jin kai ga inda suka dace.
Da yake bayyana bude taron, gwamnan jihar Kano wanda sakataren gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Baffa ya wakilta, ya yi ishara da cewa, a wani bangare na kokarin da jihar ke yi na inganta walwalar jama’a, jihar ta bai wa mata dubu biyar da dari biyu daga gundumomin jihar 484, Naira Dubu Hamsin Hamsin, yayin da aka bai wa masu fama da nakasa su dubu biyu, Naira Dubu Ashirin kowannensu, haka kuma an horas da matasa dari biyar sana'o'i daban daban, tare da basu tallafin Naira Dubu Ashirin kowannensu, da dai sauran shirye-shirye da dama.
Tun da farko a jawabin bude taron, kwamishiniyar mata da yara da masu fama da nakasa ta jihar Kano, Hajiya A’isha Saji, ta jaddada mahimmancin hadin kai da sanin makamar aiki.
Ta bukace su da su fito da dabaru, da ayyuka masu kyau da samar da sabbin hanyoyin inganta ayyukan jin dadin jama'a don samun ci gaba mai dorewa
0 Comments