Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Mata 200 Sun Amfana Da Tallafin Kudade Daga Gidauniyar BSK Foundation.

Mata 200 Sun Amfana Da Tallafin Kudade Daga Gidauniyar BSK Foundation.

Kimanin Mata 200 da suka fito daga sassan karamar hukumar Batagarawa ne suka amfana da Tallafin kudade don bunkasa kananan sana'o'i daga Gidauniyar "BSK Foundation Katsina."

Taron bada tallafin wanda ya gudana a Sakateriyar karamar hukumar Batagarawa a ranar Alhamis din nan, ya faranta ran Matan da suka amfana ba kadan ba, kamar yadda wasu daga cikinsu suka bayyana KatsinaTimes.

Da yake jawabi a yayin bada Tallafin, shugaban Gidauniyar ta BSK Foundation, Alhaji Babangida Sani Dandagoro, ya bayyana wannan Tallafin a matsayin wanda ya saba yi daga cikin aljihunsa, kuma yanzu haka ya fara shirin bayar da wani Tallafin nan gaba kadan wanda ya kunshi Maza da Mata baki daya.

Alhaji Babangida, ya kuma bayyana bada Tallafin a matsayin wanda ya koya daga kungiyar Gwagware Foundation, wanda Gwamnan jihar Katsina ya samar tun kafin zamansa gwamnan jihar.

Manyan Baki sun gabatar da jawabi a wajen, inda kowanensu ya yaba wa shugaban wannan gidauniya kan wannan hubbasawa da ya yi ta tallafawa Mata Zalla da jarin bunkasan kananan sana'o'insu, wanda kaitsaye za a iya cewar gina al'umma ne, duba da yadda dawainiyarsu da ta 'yanyansu musamman mata ke yawan haye masu, amma a haka suke da karfin halin iya tattala kananun kudade har su zama manyan kudade.

Wadanda suka halarci taron bada Tallafin kuma suka yi Jawabi a wajen sun hada da: Uwar gidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Radda wadda ta samu Wakilci mai taimaka mata ta musamman Hajiya Sa'adiyya Nasir, Shugaban karamar hukumar Batagarawa honorabul Bala Garba Tsanni, Uwar gidan Shugaban karamar hukumar Batagara, Hajiya Shafa'atu Garba Tsanni, CEO na Gwagware Foundation Alhaji Yusuf Aliyu Musawa, Mallamawan Katsina Hakimin Batagarawa Alhaji Dikko Dalhatu wanda ya samu wakilcin Alhaji Muttaka Magaji Dandagoro, Mai ba gwamna shawara kan sha'anin Siyasa Alhaji Ya'u Umar Gwajo-gwajo wanda ya samu wakilcin Galadiman kasar Hausa, mai ba gwamna shawara kan ci gaban Birane da Al'umma, Honorabul Abubakar Amadi Tsanni.

Sauran sun hada da: Alhaji Lawal Bagiwa, Danmajalissar Tarayya mai wakiltar Rimi/Batagarawa/Charanci wanda ya samu wakilcin Honorabul Sani Danlami Batagarawa, Honorabul Murtala Usman Banye, Barden Katsina Hakimin Ajiwa Alhaji Bello Usman Nagoggo wanda ya samu wakilcin Alhaji Bello Sani Magaji Jino, Magaddai, Shugaban Jam'iyyar APC na karamar Hukumar Alhaji Sahalu Bambami, masu ruwa da tsaki a jam'iyyar da sauransu.

Post a Comment

0 Comments