Hukumar Kula Da Almajiranci Da Ilimin Yaran da ba sa Zuwa Makaranta ta ce sama da Almajirai miliyan 30 ne ke gararanba a titunan kasar nan.
Sakataren zartarwa na Hukumar Dakta Mohammad Sani Idris ya bayyana haka a wajen taron yini daya da hukumar kidaya ta kasa tare da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Nassarawa suka shirya a garin Lafia babban birnin jihar.
Dakta Muhammad Sani Idris ya ce hukumar na hada gwiwa da gwamnati a dukkan matakai domin kawar da barace baracen yara akan tituna, da nufin inganta rayuwarsu ta hanyar tabbatar da ganin sun sami ilimi addini da na boko a fadin kasar nan.
Ya kuma yi nuni da cewa, nan da makwanni biyu masu zuwa hukumar za ta kaddamar da wani shiri da zai sami halartar mahaddata Alkur’ani mai girma su dari uku da hamsin a jihar Kaduna.
A nasa bangaren, shugaban hukumar kidaya ta kasa Alhaji Nasir Isa Kwara, ya ce an shirya taron ne domin samar da mafita da dabaru kan kalubale iri daban-daban na sauyin yanayi da tsaro, da yaran da ba sa zuwa makaranta a shiyyar Arewa ta tsakiya.
A jawabinsa, Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya yi kira da a hada karfi da karfe wajen rage yawan Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta a kan titunan da ke fadin kasar nan.
Gwamnan wanda ya bayyana taron a matsayin abin ya dace, ya bayyana cewa batutuwan da suka shafi yaran da ba su zuwa makaranta da almajirai sun kasance babban abin damuwa da ke bukatar hada kai da bangarori daban-daban don shawo kan matsalar.
Ya ce gwamnatin jihar na kokarin samar da makarantu a kananan hukumomi uku na jihar domin rage yawan almajirai da ke gararanba a tituna, ya kuma yi kira ga iyaye da sauran jama’a da su guji tura ‘ya’yansu neman ilimin addini ba tare da wani tanadi na musamman ba.
Taron na yini guda kan al'amuran jama'a, da tsaro, da kuma sauyin yanayi, an yi shi ne da nufin samar da hanyoyin da za a bi don magance matsalolin yaran da ba su zuwa makaranta,da Almajirai da masu rauni a kan tituna.
0 Comments