Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo Ya Bada Tallafin Bas Mai Kujeru 60 Ga Jami'ar FUDMA


Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo Ya Bada Tallafin Bas Mai Kujeru 60 Ga Jami'ar FUDMA

Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) ta gudanar da taron yaye ɗalibai a karo na 9, a inda ta samu wani karamcin kyauta ta musamman daga Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, a inda ya bai wa jami’ar motar bas mai cin mutum 60.

Sabuwar motar bas ɗin za ta sauʙaʙa ʙalubalen sufuri ga ɗalibai, waɗanda da yawa daga cikinsu ke kokawa bisa ʙarancin motocin zirga-zirga. 

A yayin bikin, shugaban jami'ar ta FUDMA, Farfesa Armaya'u Bichi, ya bayyana matuʙar jin daɗin jami'ar ga irin gudunmawar da Farfesa Gwarzo ya bayar.

"Wannan motar bas ɗin za ta zama babbar ʙadara ga ɗalibanmu, tare da ʙarfafa su wajen halartar azuzuwa da kuma shiga cikin harkokin karatu," in ji Farfesa Bichi.

"Muna matuʙar godiya da jajircewar Farfesa Gwarzo na tallafawa ilimi a aikace ta hanyoyi masu tasiri.

Ɗalibai da ma'aikatan da suka halarci taron sun yi nuna jinɗaɗin su bisa yadda wannan kyautar sabuwar motar bas za ta yi tasiri ga rayuwar su ta tau da kullum a harabar jami'a. 

Karamcin na Farfesa Gwarzo abin koyi ne kuma tunatarwa ne mai tasiri ga yadda tallafin zai iya haɓaka ilimi da ba da gudummawa ga nasarar ɗalibai.

Post a Comment

0 Comments