Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Ya kamata mu haɗa kanmu don ci gaban rayuwar al'ummar mu Inji--- hon Albani Samaru


Daga Idris Umar, Zariya

Honorabul Abubakar Jamil Albani shine ɗan takarar kujerar shugaban karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna kuma ɗan majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar gundumar Basawa a karamar hukumar Sabon Gari karkashin jam'iyyar APC.

Ya baiyana neman haɗin kan al'ummarsa ne jim ƙaɗan bayan ya jefa kuri'arsa a mazabarsa dake makarantar Sa'eedu Primary School dake garin Samaru mai lamba ( 0.12).

Honorabul Albashi na ɗaya daga cikin matasan yan siyasa masu jini a jika a faɗin jihar Kaduna .

Kuma ya nuna matukar jin daɗi da yabo da godiya ga jama'ar karamar hukumar Sabon Gari bisa yadda suka fito kwansu da ƙwarkwatarsu suka baiwa Jamɓiyar APC goyon baya a wannan zaɓe.

Bisa hakane ya nemi alfarma ga jama'arsa da suzo a dunkulewa guri ɗaya don tunkara tare da magance dukkan wani ƙalubalen dake gaban karamar hukumar tasu ta Sabon Gari.

Yace mu yafewa juna tunda yanzu maganace ta nuna kishin al'ummarka da kawo abinda zai taimaka masu ba tare da nuna ƙabilanciba don haka mu haɗa kanmu don ci gaban rayuwar al'ummarmu,

Ƙarshe ya tabbatar da cewa da ikon Allah Jamɓiyar APC zataci gaba da yiwa al'umma hidima ba tare da yin kasa a guiwa ba.

Honorabul Albani ya yabawa Gwamna jihar Kaduna sanata Uba Sani bisa gudummawar da yake bayarwa ga al'ummar jihar Kaduna ta bangaren harkar Ilimi da tsaro da harkar lafiya.

Bincike ya nuna Honorabul Albani yanzu haka ya zama uba a karamar hukumar Sabon Gari duk da ƙarancin shekaru.

Kuma jama'a da yawa sun shaideshi da girmama na gaba dashi tare da neman sulhu a tsakanin mutane.

Yayin da hukumar zabe ta jihar Kaduna ta shelanta cewa jamɓiyar APC ta lashe kujeru 23 na shugabancin ƙananan hukumomi da kansiloli na dukkan jihar Kaduna dubban mutane ne suka rinƙa yin dafifi a gidan Honorabul Albani don taya shi murnar samun nasara ciki harda makarantun Islamiyoyi da kungiyoyi da makarantu masu zaman kansu da limaman addinai.

Hakan ne ya nuna cewa dan takarar na yin abin da ya kamata a cikin al'ummarsa saɓanin wasu guraren da aka rinka bin wasu yan takarar da jifa wanda hakan ya nuna basu dauki salon siyasa irin ta Honorabul Albani ba.

Post a Comment

0 Comments