Jami'an hukumar zaben jihar Kano na ci gaba da tattara sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka gudanar a yau Asabar.
A wasu rumfunan zaɓen an kammala zaɓen tun da safe, bayan da a wasu wuraren aka samu ƙarancin fitowar masu zaɓe.
Jam'iyyar APC mai hamayyar jihar dai ba t shiga zaɓen ba, haka ita ma rundunar 'yan sandan jihar ba ta shiga za ben ba saboda umarnin kotun tarayya da ya hanata shiga zaɓen.
Jami'an hukumar Karota da na Vigilante ne dai suka bayar da tsaro a lokacin zaɓen.
0 Comments