Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Hayakin Motocin Hakimai na Zubar da Martabar Sarauta a Kudan


Hayakin Motocin Hakimai na Zubar da Martabar Sarauta a Kudan

Daga Idris Umar, Zariya

A cikin satin da ya gabata, wani daga cikin Hakiman karamar hukumar Kudan da ke jihar Kaduna Alhaji Aminu Muhammad Ashiru ya bayyana damuwarsa dangane da mawuyacin halin da suka ciki , musamman a bangaren Motocin da suke hawa a halin yanzu.

Hakimin, wanda ya bayyana cewa motocin da aka ware musu sun lalace matuƙa, har ta kai ga duk lokacin da za su halarci taro sai sun beye motocin saboda kunyar irin halin da suke ciki.

A taron jin ra'ayin jama'ar karamar hukumar da ya gudana a yan kwanaki ƙadan da suka gabata.

Hakim ya bayyana damuwarsa ne kai tsaye ga shugaban karamar hukumar Kudan, Hon. Dauda Iliya, yana mai cewa wannan matsala na buÆ™atar kulawa ta gaggawa domin ta shafi mutuncin sarautar gargajiya da kuma aikin da suke yi wajen taimaka wa al’umma.

Binciken da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa ba motocin kawai ne suka lalace ba, har ma da gidajen Hakiman da dama sun lalace, suna buƙatar gyara cikin gaggawa. Idan aka kwatanta da wasu ƙananan hukumomi a jihar, lamarin na Kudan abin takaici ne.

Wasu daga cikin mazauna yankin na ganin cewa Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, watakila bai san da wannan hali na kaskanci da wasu Hakiman ke ciki ba. Sun bayyana cewa abin kunya ne ace a wannan zamani, Hakimi yana hawa mota mai fitar da hayaki, wanda hakan ke rage kimar sarauta a idon jama'a.

“Duk da irin gudummawar da sarakunan ke bayarwa wajen samar da zaman lafiya da ci gaban al’umma, bai kamata a bar su cikin irin wannan hali ba,” inji wani mazaunin yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban karamar hukumar, Hon. Dauda Iliya, ya yi alkawarin gyara motocin nan bada jimawa ba. Sai dai tambayar da jama’a ke yi ita ce: Me zai hana Gwamnan Jihar Kaduna ya samar musu da sababbin motocin aiki?

Al’umma na dakon ganin yadda gwamnati za ta maida hankali kan wannan batu da ke ci wa sarakuna da jama’ar yankin tuwo a kwarya.

Post a Comment

0 Comments