Zaria Youth Association ta ziyarci Sarkin Zazzau
Daga Idris Umar,Zariya
kungiyar matasan Zaria wato Zaria Youth Association karkashin jagorancin shugaban kungiyar Rt. Comr Yusuf Bello Umar (Limamin Matasa) ta kai ziyarar gaisuwa tare da neman sanya albarka ga mai martaba Sarkin Zazzau Amb. Mal. Ahmad Nuhu Bamalli a fadar shi dake birnin Zaria.
A yayin da yake jawabi a madadin kungiyar, shugaban kungiyar ya fara da gaisuwa da nuna godiya ga mai martaba Sarkin Zazzau daya tarbi kungiyar cikin aminci da karamci.
Limamin matasa ya gabarwa mai martaba Sarkin Zazzau nasarori da manufofin kungiyar, kama tun daga kan horas da matasa a fannonin sana'o'i da dama domin dogaro da kan su da kuma wayar da kan al'umma domin samar masu da gobe mai kyau domin cigaban al'ummar Zaria gaba daya.
Mai martaba Sarkin Zazzau, Amb. Mal. Ahmad Nuhu Bamalli ya yaba tare da nuna jin dadin shi a bisa wannan ziyara da wannan kungiya mai albarka ta kawo mashi. Sannan ya yaba mata kan ayyukan cigaba da take yi inda yayi alqawarin bata gudummuwa Dari bisa Dari domin ta cigaba da aiwatar da wadannan ayyukan alkhairi.
"Naji dadi da samun matasa masu tunanin kawo cigaba a kasar Zazzau kamar ku, a madadin masarautar Zazzau zamu yi duk mai yiwuwa wajen ganin mun karfafa maku gwuiwa ta kowane fanni domin ku cigaba da gudanar da wadannan ire-iren ayyuka" Inji Sarkin Zazzau Bamalli.
Daga karshe, Sarkin ya yabawa Shugaban gidauniyar I-DANRAKA CARE FOUNDATION Mal. Isiyaku Mustapha Danraka bisa namijin kokarin da yake yi na tallafawa wannan kungiya da sauran al'ummar birnin Zazzau. Inda ya shawarci sauran masu hali da su shigo su bada nasu gudummuwar. Sannan ya kuma sanyawa kungiyar albarka tare da bada shawarwari na karfafa gwuiwa da alqawura na alkhairi.
0 Comments