Shugaban Hukumar Zaɓe Ta Jihar Bauchi, Ahmad Makama, Ya Rasu
Shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi 'Bauchi State Independent Electoral Commission' (BASIEC), Alhaji Ahmed Makama Hardawa, ya kwanta dama.
Makama, wanda ya kasance tsohon babban Kwamishinan zaɓe na hukumar INEC a jihohin Taraba da Nasarawa, ya rasu ne a jiya Talata 29 ga watan Yuli na 2025, a Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad shi ne ya sanar da rasuwar nasa, inda ya nuna alhini da juyayin rashin, tare da misalta hakan a matsayin rashi ga jihar da ma ƙasa.
0 Comments