Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Gwamnonin Arewa Maso Yamma Sun Ayyana Talatar Gobe a matsayin ranar huta Don Karrama Marigayi Shugaba Buhari


Gwamnonin Arewa Maso Yamma Sun Ayyana Talatar Gobe a matsayin ranar huta Don Karrama Marigayi Shugaba Buhari 

Gwamnonin Jihohin Arewa maso Yamma sun ayyana Talata, 15 ga Yuli, 2025 a matsayin hutu na musamman a dukkan jihohin yankin domin girmama tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin London.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma kuma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, yana mai bayyana jimami da alhini dangane da rasuwar marigayin.

“Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma ta karɓi labarin rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Janar Muhammadu Buhari (rtd), da matuƙar bakin ciki da alhini. Ya kasance uba, jagora kuma gwanin alfahari ga yankin Arewa maso Yamma,” in ji sanarwar.

Gwamna Radda ya bayyana cewa hutun na musamman da aka ayyana yana nuna girmamawa da yabo ga marigayin wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa ƙasa da al’umma hidima da gaskiya da rikon amana.

Haka kuma, sanarwar ta tabbatar da cewa ana sa ran za a kawo gawar marigayi shugaba Buhari zuwa Katsina da misalin ƙarfe 12 na rana ranar Talata, yayin da aka shirya jana’izarsa da ƙarfe 2 na rana a mahaifarsa Daura.

Kungiyar ta miƙa ta'aziyyarta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, iyalan marigayin, gwamnatin Jihar Katsina da daukacin al’ummar Najeriya bisa wannan babban rashi da aka yi.

“Ina roƙon Allah ya gafarta masa, ya saka masa da Aljannah Firdaus, ya kuma ba iyalansa da abokansa da dukkan al’ummar Najeriya haƙurin jure wannan babban rashi,” in ji sanarwar.

Post a Comment

0 Comments