Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Gwamna Uba sani ya bayyana kokarin sa domin bunkasa Harkokin Noma a jihar Kaduna.


Gwamna Uba sani ya bayyana kokarin sa domin bunkasa Harkokin Noma a jihar Kaduna.

Gwamna Uba Sani ya bi sahun mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, GCON, da takwarorinsa gwamnoni, da sauran masu ruwa da tsaki a taron harkar noma, domin kaddamar da tsarin dabarun noma na kasa (NAPM) a hukumance a dakin taro na Banquet Hall dake fadar shugaban kasa, Abuja.  

Mataimakin shugaban kasa ya samu wakilcin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Sanata Ibrahim Hadejia. 

 A nasa jawabin, Gwamna Uba Sani ya bayyana wasu nasarorin da aka samu a harkar noma da kuma tsare-tsare da gwamnatinsa ke bi wajen tabbatar da samar da abinci da kawo sauyi ga tattalin arzikin jihar Kaduna.

 Ya ce kaddamar da NAPM ya zo kan lokaci kuma yana samar da tsarin hadin gwiwa don daidaita manufofi, daidaita zuba jari, da kuma musayar muhimman bayanai don yanke shawara mai kyau a fannin noma.

Post a Comment

0 Comments