Babu kamshin gaskiya a batun gadon wasiku 300 ga sabon muƙaddashin jami'ar Ahmadu Bello
Daga Idris Umar,Zariya
Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ta karyata wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta da wani shafin yanar gizo na Education Monitor ya wallafa a ranar Alhamis, 30 ga Afrilu, 2025.
Rahoton, wanda ke ɗauke da taken “Sabon VC na ABU na 14, Farfesa Adamu, ya karɓi ragamar jagoranci, tare da gadon wasiku 300 da ba a duba ba,” ya fito daga marubuci Adamu Isah Waziri.
Hukumar ta bayyana cewar wannan take ba gaskiya ba ne domin babu wani lokaci da sabon Mataimakin Shugaban Jami’a (Vice-Chancellor), Farfesa Adamu Ahmed, ya ambaci irin wannan magana a jawabinsa yayin bikin mika mulki daga hannun Farfesa Kabiru Bala a cewar hukumar
A gaskiya, sabon VC ya hau ofis ne cikin tsari, ba tare da wata wasika ko aiki da bai kammala ba. Babu wani abu da ya gada da ba a kula da shi ba. Tsohon VC, Farfesa Kabiru Bala, ya tabbatar da cewar duk wata matsala ko aiki da ke akwai an kammala su kafin saukarsa daga kujerar shugabanci.
An kuma bayyana cewa, shirin mika mulki ya fara watanni biyu kafin bikin ranar 30 ga Afrilu, 2025, inda aka gudanar da tarurruka da ayyukan da suka tabbatar da cikakken mika mulki ba tare da wata matsala ba. Wannan ya sa bikin ranar 30 ga Afrilu ya zama na al’ada kawai.
Sabon VC, Farfesa Adamu Ahmed, ya gode wa Farfesa Kabiru Bala bisa hadin kai da goyon bayan da suka yi masa a lokacin sauyin mulki. Haka kuma, ya yaba da tawagar manyan jami’ai da ya tarar da su a ofis, ciki har da mataimakan VC guda uku da sauran manyan jami’an gudanarwa.
0 Comments