Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Yadda (mai Saba'in) ke taimakawa al'umma a garin Samaru



Yadda (mai Saba'in) ke taimakawa al'umma a garin Samaru 

Daga Idris Umar Zariya

Al'ummar garin Samaru na ƙara godiya da fatan alheri ga matashinnan da ake kira (Sani Halliru mai Saba'in) wanda ya dukufa wajan taimakawa jama'ar garin Samaru da kewaye.

Yayin da matashin ke zantawa da manema labarai a lokacin fitowarsa daga wani taro da wata kungiya mai suna AMAS TRUSTEE YOUTH FORUM BASAWA CONSTITUENCY Suka shirya a bubban ɗakin taro na makarantar sakandaren Bomo a garin Bomo karamar hukumar Sabon Gari.

Mai Saba'in ya tabbatar da cewa duk abin da yakeyi ya gaji abin mahaifinsa ne mai Suna Sani Dan Sanda Samaru wanda Allah yayi masa rasuwa shekarun baya.

Malam Sani Dan'Sanda bincike ya nuna cewa Dan'Sanda ne mai taimakon jama'a bakin aikinsa dare da rana.

Matashin yace yana yin sadaka da kyauta ne saboda samun yardar Allah da neman gafara ga iyayensa .

Yanzu bicike ya tabbatar da cewa matashin mai rajin bayar da taimako ya kai daukin gyara wata hanya data lalace a (junction din layin Zana hanyar Sabon Birni karkashin kungiyarsa mai suna (Mai Saba'in initiative movement)

Binciken ya nuna cewa shi matashin bashi da wata manufa ta siyasa illa son taimakon al'umma.

Wani fata kuke mashi

Post a Comment

0 Comments