Daga Idris Umar,Zariya
Tun farko shugaban Dakta Muhammed Mu'azu,Mukaddas ya bayyana irin yadda hukumar nasa take gabatar da aiyukanta a gaban mai girma sarkin na Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli da sauran mambobin masarautar ta Zazzau.
Shugaban yace,hukumar su hukumance dake kawo Ci Gaban Al'umma da Zamantakewa a Jihar Kaduna wato (KSCSDA) wata hukuma ce ta gwamnati a Jihar Kaduna wadda ke da nufin inganta rayuwar al'ummomi a kauyuku. Hukumar tana mai da hankali kan aiwatar da ayyukan da zasu inganta ci gaban al'umma da rage talauci ta hanyar samar da kayan more rayuwa da ayyukan zamantakewa na asali. Tana aiki tare da hukumomin kananan hukumomi, mambobin al'umma, da sauran masu ruwa da tsaki domin gano, tsara, da aiwatar da ayyukan ci gaba kamar hanyoyi, samar da ruwan sha, cibiyoyin kiwon lafiya, ilimi, da tsabtace muhalli.
Hukumar KSCSDA tana kuma bada muhimmanci wajen ba da damar shiga ga al'umma wajen yanke shawarar ayyukan ci gaba. Haka kuma, tana yin hadin gwiwa da kungiyoyin ci gaban kasa da kasa, kamar Bankin Duniya da Gwamnatin Tarayya ta Najeriya, domin samar da kudade da aiwatar da ayyukanta. Ta hanyar wadannan kokarin, tana nufin rage talauci, inganta rayuwar al'umma, da bunkasa ci gaba mai dorewa a yankunan da ba su ci gaba ba a cikin jihar.
Bayan gabatar da jawabin nasa ne mai martaban Sarkin Zazzau yayi masa barka da zuwa tare da tawagarsa kuma har yayi masa jinjina bisa ƙokarin da ya bayyana na hukumar a gaban Sarki da yan majalisarsa.
Daga karshe sarkin ya nemi hukumar ta kawowa masarautar dauki akan ƙalubalen da masarautar ke fuskanta akan karancin ruwa a halin yanzu.
Shugan ya amsa koƙen masarautar tare da alƙawarin daukar mataki akan lamarin cikin gaggawa.
Bayan mai martaba ya kammala karbar bakuntar shugaba ne wakilimu ya Zanta da shugaban don jin ta bakinsa akan ziyarar da ya kawo a yau ga masarautar ta Zazzau.
Dakta Mukaddas shine shugaban hukumar ta (KSCSDA) ya bayyana wa wakilan kafafen yaɗa labarai cewa ziyarar tasu ta ƙunshi sada zumunci ne da neman haɗa al'umma da hukumar tasu don samun moriyar da hukumar ke bayarwa ga al'ummar jihar Kaduna.
Kuma ya bayyana irin nasarorin da hukumar kumar ta samu a yanzu haka Yace,
Ɓangaren kiwon Lafiya hukumar tasu ta gida asibitoci guda 13 wanda maza da mata guda 12,498,000 suke amfana a yanzu haka.
A ɓangaren gyaran makarantu kuma shugaban yace hukumar tasu ta gyara azuzuwa guda 77 wanda a ƙalla ɗalubai 90,8,23,000.ke amfanar dasu yanzu haka.
Shugaban ya kara tabbatar da gina Rijiyar Burtsatse guda 81 wanda mutane kimamin 92,000 suke amfana da su a yanzu haka.
A ɓangaren tsaftace muhalli kuwa shugan ya bayyana cewa hukumar tasu ta kwashi masu shara kimamin mutum 5,112000.
Haka zalika shugaban yace hukumar tasu ta bayar da tallafi kayayyakin sana'a ga kungiyoyin Mata da maza kimamin su 5,129,000 don inganta rayuwa.
Karshe shugaban ya tabbatar da bayar da tallafi na kuɗi Naira 1000,000 ɗaya da kuma Naira 5000,000 ga masu ƙanana sana'a a matsayin Jari ga mutane 13,3,35,000 a yanzu haka.
Karshe yayi godiya ga mai martaba sarkin Zazzau da Majalisar sa bisa karamci da aka nuna masu.
0 Comments