IAR ta shirya taron Bita da Tsare-Tsaren Bincike na Shekarar 2025 a Zariya
Daga Idris Umar, Zariya
A ranar Laraba, 23 ga Afrilu 2025, ne Cibiyar Binciken Harkokin Noma (IAR), Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, ta gudanar da Taron Bita da Tsare-Tsaren Bincike na Shekara (ARRPM) — taron da ke da nufin duba ci gaban da aka samu, musayar sabbin dabaru, da daidaita binciken noma da manufofin cigaban kasa.
An bude taron da tarbar manyan baki masu daraja. Daraktan Cibiyar IAR, Farfesa Ado Yusuf, ya gabatar da jawabinsa na maraba cikin hikima da fasaha, wanda ya sa aka fara taron cikin nishadi da azanci. Ya jaddada muhimmiyar rawar da IAR ke takawa wajen kawo sabbin hanyoyin noma da dorewar cigaba a fadin Najeriya.
An kuma saurari jawaban maraba daga baki na musamman kamar su, Mukaddashin Sakataren Hukumar Binciken Harkokin Noma ta Najeriya (ARCN), Farfesa Bello Zaki (wanda Daraktan NAERLS, Farfesa Yusuf Sani, ya wakilta), Shugaban Hafsoshin Tsaron Najeriya Janar Christopher Musa, Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, Daraktan NAPRI Farfesa Muhammad Hassan, Wakilin ICRISAT a Najeriya, da Mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar Ilimi ta Tarayya Zariya, da sauransu.
Jawabin Shugaban Taro wanda Shi ne Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Kabir Bala, ya kasance cikin kwarewa da nuna gogewar jagoranci da ilimi.
Daya daga cikin muhimman abubuwan taron shi ne gabatar da jawabi na musamman daga Hajiya Bintu Muhammad Nakudu (wakiliyar Mr. Samuel Adegahi Musa), Darakta Janar na Majestik Farms, Jihar Jigawa. Ta tattauna sosai kan sauya fasalin noma, kimar amfanin gona da rawar da kamfanonin masu zaman kansu ke takawa wajen samar da abinci mai yawa. Taken jawabin ya kasance "Inganta Samar da Abinci da Tattalin Arziki ta Hanyar Kirkire-Kirkiren Noma", wanda ya kalubalanci mahalarta da su fitar da sabbin hanyoyin zamani wajen cimma nasara.
An rufe zaman bude taron da godiya mai ratsa zuciya daga Farfesa Nafiu Abdu, Mataimakin Darakta na IAR, wanda ya nuna godiya ga baki, ma’aikata da duk masu hadin guiwa da suka goyi bayan ci gaban harkar noma.
Daga bisani aka ci gaba da gudanar da zaman bitar sassa daban-daban guda biyu, inda kowanne shirin bincike da sassan cibiyar suka gabatar da nasarorin da suka samu da kuma shirye-shiryen nan gaba. Haka kuma an samu gabatarwa daga abokan hulda da hadin guiwa kamar su ICRISAT, Premier Seed, NIMET, NAERLS, NAPRI, da FRIN, wadanda suka kawo mahimman bayanai.
Dakin taron cike yake da manyan baki da suka hada da wakilan ADPs, Dekan-dekan da Daraktoci daga ABU, tsoffin Daraktoci Janar na IAR, da daukacin kwararrun masu bincike da ma’aikatan IAR.
Taron ya kasance mahaɗa ta tunawa da cigaba da kuma fatan alheri — inda aka duba nasarorin bincike na baya da kuma fitar da sabbin hanyoyi masu karfi don ciyar da harkar noma gaba a Najeriya. Wurin haduwar kimiyya da manufofi ne, inda ainihin matsalolin da manoma ke fuskanta suka zama ginshikin sabbin bincike. Da sabuwar himma da hadin kai, mahalarta sun tattauna sabbin mafita don sauya fuskar noma, taimaka wa manoma da kuma kare rayuwar al’umma.
Taron zai ɗauki kwanaki 2 ne kasance mafi tasiri yayin da za a gudanar da Taron Zonal REFILS, inda za a mayar da hankali kan hadin gwiwa tsakanin bincike da manoma ta hanyar ingantattun hanyoyin yada ilimi da fasahar zamani.
0 Comments