Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Har yanzu gidauniyar Ajoke Ayisat Afolabi Foundation na taimakawa al'umma Inji ----- Adama Shehu Aliyu


Har yanzu gidauniyar Ajoke Ayisat Afolabi Foundation na taimakawa al'umma Inji ----- Adama Haruna Abdul-Malik

Daga Idris Umar,Zariya

A cikin wannan makone tawagar yan jaridu daga gidajen yaɗa labarai daban daban suka kai ziyarar gani da ido cibiyar Ajoke Ayisat Afolabi Foundation dake a cikin garin Hanawa ta ƙaramar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Ziyarar kafafen yaÉ—a labarai ya kunshi abubuwa guda biyu ne.

Na farko jin yadda wannan gidauniyar ke gabatar da aiyukanta ga al'umma musamman a halin da ake ciki na matsin rayuwa.

Na biyu kuma amsa tambayoyin da suka shafi kokarin da ita gidauniyar ke gabatarwa ga al'umma a irin wannan lokaci.

Tun da farko dai Hajiya Adama ce ta karɓi bakuncin tawagar manema labaran tare da yin marhaban-lale da ziyarar.

Hajiya  Adama tana cikin shuwagaban wannan gidauniya kuma a cikin jawabinta ta tabbatar da cewa gidauniyar su ta kafu sama da shekaru 10 baya .

Adama ta baiyana irin ayyukan da gidauniyar ke gabatarwa kamar haka.

Tace na farko dai cibiyar an kafata ne don taimakon masu rani yara da manya.

Ta kara da ciwa akwai ɓangarori da dama daga ciki akwai sashin makarantar yara akwai sashin koyar da sana'o'i sannan akwai ɓangaren kiwon lafiya don taimakon masa galihu.

Hajiya Adama tace bayan irin wancan aiyukan akwai hidimar bayar da taimakon azumi ga jama'a.

Tace duk watan azumi suka dafa buhunan shinkafa don rabawa al'umar Annabi duba da halin da ake ciki a yanzu.

Tace a yanzu haka suna duba É—aruruwa marasa lafiya da suka je asibiti aka rubuta masu magani kuma basu da kuÉ—in siya muka duba takardarsu mu basu maganin da aka rubuta masu ko mu basu kuÉ—i suje su siya komin tsadarsa.

Bisa haka ne Hajiya Adama tayi kira da babban murya cewa duk mai son taimakawa al'umma to yazo (Ajoke Ayisat Afolabi Foundation) hanya a bude take don haÉ—a hannu.

Kuma tayi kira ga al'ummar Musulmai cewa mafi girman taimakon da wannan gidauniyar ta samu daga hannun wani wanda ba Musulmi bane don haka tace ya dace musulmi su zabura wajan yin aikin alheri irin wannan.

Hajiyar ta baiyana matsalar tattalin arziki ƙasa da ake fama dashi a matsayin abin dake kasowa cibiyar cikar da yasa taimakawar gidauniyar ya rabu matuka da kashi wajan 5 cikin 10 amma tace suna godiya ga Allah kuma zasu ci gaba.

Mai gidan Hajiya Adama  malam Shehu Aliyu shima ya nuna jin daÉ—insa game da ziyarar gani da idanu da gidajen jaridu suka kawowa gidauniyar tasu.

Kuma a jawabinsa na godiya ya tabbatar da cewa gidauniyar zata ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin ikon Allah.

Kuma yayi godiya ga uban gidauniyar bisa ƙoƙari da yakeyi yayi fatan alheri gareshi da sauran masu taimakawa gajiyayyu.

A cikin ziyarar ne muka sami zantawa da wata mata da ta sami tallafin magani daga wannan gidauniyar ta Ajoke Ayisat Afolabi Foundation akan rashin lafiya ciwon hawan jini da ciwon suga har ta tabbatar da cewa yanzu haka gidauniyar ta siya mata gadon kwanciya na ƙarfe don kokarin sama mata lafiya.

Shima malam Muhammadu mai lalurar ciwon ƙafa shima yayi matukar godiya bisa tallafi da gidauniyar take bashi a yanzu hakan yasa yayi masu fatan Alheri baki ɗaya.

Post a Comment

0 Comments