Gwamna Yusuf Ya Umarta Masarautu Hudu na Kano Da Su Fara Shirye-shiryen Bukukuwan Sallah Durbar
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci dukkanin masarautu hudu na jihar da su fara shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Sallah Durbar, domin tabbatar da cewa 'yan kasa da baƙi za su more wannan lokaci na bukukuwa. Wannan umarni na gwamnan ya fito ne daga wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar bayan wani taron hawan sallah da aka gudanar da Sarakunan Kano a fadar gwamna.
Gwamnan ya bayyana cewa, al'adar Sallah Durbar ta zama daya daga cikin al'adun gargajiya da 'yan Kano ke matuƙar jindadi da ita, inda ake sanya sabbin kaya, cika tituna da kallon Sarakunan suna hawa dawaki, da kuma musayar gaisuwa. Gwamna Yusuf ya jaddada cewa gwamnatin sa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an gudanar da bukukuwan cikin lumana, tare da tabbatar da tsaro ga al'umma.
A cewar gwamnan, za a kaddamar da Majalisar Masarautar Kano a watan Afrilu, inda za a sanar da ka'idojin gudanarwar ta. Ya kuma yabawa kyakkyawar dangantaka da girmamawa da Sarakunan jihar, wanda ya ce yana daga cikin abin tarihi a jihar Kano.
A jawabinsu, Sarakunan Kano sun yaba da gudunmawar da Gwamna Yusuf ya bayar wajen samar da takin zamani da kuma inganta ababen more rayuwa kamar ilimi, lafiya, da hanyoyin mota a cikin yankunansu.
0 Comments