Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Gwamma Uba Sani Ya Ba Da Umurnin A Gaggauta Biyan Malam Mohammed Bature Jibrin Hakkokinsa


KIRA GA MAI GIRMA GWAMNAR JIHAR KADUNA 

Mal Mohammed Bature Jibrin. Quantity Surveyor ne yayi karatu a ABU Zaria yafito da first class yayi NYSC din shi a kaduna. Saboda jajircewan sa aka bashi Aiki a Kaduna State, Daga 1987 zuwa 2020, kafin ya bar Aiki sai da ya kai matsayin Director a Ministry of Works, Housing and Transport.

Yana kan aikin sa sai wancen Gwamnatin ta sauke shi a cikin shirinta na rage ma’aikata ba tare da biyan sa hakin saba ko kwabo ba'a bashi ba, Ba fansho ba Garaduti shekara biyar kenan.
Tunda yabar aiki, shine Mai sharan masallaci kuma ladanin Massalacin dake SkyPet layin Mai Anguwa Abdullahi road Rigachikun. Wani lokacin ma Yana limanci.

Ya samu tabin hankali saboda rashin biyansa hakkin sa da Gwamnatin da ta wuce batayi ba har yakai da an dakatar dashi daga limancin da yakan taimaka wasu lukutan.

A yanzu Yana karban magani a Asibitin masu lalurar kwakwalwa dake Barnawa.

Dan Allah a chigaba da yadawa har sai ya Kai gaban Gwamna, Kowa yasan Gwamnan mu '
Mai Girma Gwamna Sanata Uba Sani. Irin abinda yake nema kenan Dan ya taimaka.

Ga nunban shi

 07060608330
 Ga na matar shi

 07062621609

Duk Mai San ganin shi da taimako Kuma, Yana iya kiranshi. 

Don Allah Jama'a a taimaka da share

Bayan daukar matakin yaɗa wannan bayanai na wannan bawan Allah ne sai gashi rahotanni suna nuna cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu ga rahotan abin da ya biyo bayan rahoton da ya karaɗe shafukan sada zumunta ga rahotan nan a ƙasa


Gwamma Uba Sani Ya Ba Da Umurnin A Gaggauta Biyan Malam Mohammed Bature Jibrin Hakkokinsa

A jiya ne Gwamna Uba Sani ya nemi a kawo masa Malam Mohammed Bature Jibrin wanda hotunansa suka karade shafukan sada zumunta cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta kore shi aiki a shekara ta 2020 kuma ba a biya shi hakkokinsa na aiki ba wanda hakan ya yi sanadiyar samun tabin hankali. 

Yanzu haka dai Gwamna Uba Sani ya ba shi hakuri, ya  kuma yi masa alheri, sannan kuma ya bayar da umurnin a gaggauta biyan shi hakkokinsa kafin nan ki makon gobe.  Sannan Gwamnan ya kira taro da Hukumar Fansho ta Jihar Kaduna don binciko duk masu matsaloli irin wannan musamman wadanda aka kore su aiki ko suka yi ritaya amma ba a biya su ba a biya su hakkokinsu 

Wani fata kukewa Sanata Uba Sani?

Post a Comment

0 Comments