Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Wata gobara ta tashi a makarantar Tsangaya (Makarantar Almajiri) taci rayuka


Wata gobara ta tashi a makarantar Tsangaya (Makarantar Almajiri) sannan ta yi ajalin mutuwar yara 17 a karamar hukumar Kaura-Namoda ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce gobarar da ta tashi a tsakar dare ta kuma raunata akalla wasu daliban makarantar su 16.

Shugaban karamar hukumar Kaura-Namoda, Mannir Haidara, ya tabbatar da faruwar lamarin ga talabijin na Channels a ranar Laraba.

Wani mazaunin unguwar mai suna malam Abdul Razak Bello ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a cikin É—akin karatu da ke makarantar Mallam Ghali Tsangaya. Ya ce gobarar ta yi muni ne saboda masara da kutuwar gero da aka ajiye a harabar makarantar.

Mazauna yankin sun ce gobarar ta tashi ne da yammacin ranar Talata kuma ta ci na tsawon sa’o’i hudu.

“Akwai kusan yara 100 daga cikinsu a gidan, bayan sun kwashe daliban, sai suka yi tunanin babu daya daga cikinsu da ya rage a cikin gidan, a lokacin da suka dawo bayan gobarar ne suka fara ganin kafafuwansu, hannayensu, sun kone ba a iya gane su ba,” inji Bello.

Ya ce an binne gawarwakin mutane 17 da aka gano a ranar Laraba.

Post a Comment

0 Comments