Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Waɗansu mutane sun tare hanyar Sakkwato


YANZU-YANZU: waɗansu mutane sun tare hanyar Sakkwato tsawon awa biyar

Rahotannin dake shigo mana a halin yanzu na nuni da cewa waɗansu mutane dake haƙar ma'adanai sun tare hanyar Sakkwato a daidai garin Maru ta jihar Zamfara tun daga misalin ƙarfe 10 na safiyar yau Alhamis har ya zuwa haɗa wannan rahoto da misalin ƙarfe 2:57 na yammaci.  

Ganau sun shaidawa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne sakamakon yadda sojoji suka ce suka kwashe wa masu haƙar ma'adanan babura. Lamarin da ya sanya masu haƙar ma'adanan suka bazama a kan tituna a daidai garin Maru suka tare hanyar baki ɗaya. 

Ganau sun shaida mana cewa dubban motoci ne da suka fito daga Sakkwato da waɗanda suka fito daga Kaduna suka yi cincirindo ko matsawa ba su iya yi ba sakamakon tare hanyar. 

Ya zuwa haɗa wannan rahoto babu wata gudunmawa da matafiyan suka samu daga jami'an tsaron soja ko na ƴan sanda.

Post a Comment

0 Comments