Kungiyar masu sayar da katako ta Zariya sun zabi Alhaji Abaye a matsayin shugaba
Daga Idris Umar, Zariya
Shugaban zaɓe Kwared Jibiril Salihi jagoran kungiyar Majilisar matasa ta ƙasa reshen ƙaramar hukumar Sabon Gari ya baiyana Alhaji Ahmadu Abaye a matsayin sabon shugaban kungiyar masu sayar da Katako ta Zariya da kuri'u 237 inda ya yi nasara a kan masu takara da shi mutum biyu.
An gudanar da zaben ne a kusa da makarantar Era International College Railway, Zariya a ranar Asabar.
Wasu daga cikin jami'an da aka zaba sun hada da Yunusa Gambo Garba a matsayin mataimakin shugaba da kuri'u 316, Ibrahim Alhassan a matsayin babban sakatare da kuri'u 283 da kuma Haruna Halilu a matsayin mataimakin sakatare.
Alhaji Jazuli shine Sakataren Kudi, Abdullahi Usman a matsayin Ma'aji, Abdullahi Abdulhadi shine 'Auditor' da Nura Abubakar a matsayin Mai kula da hulda da jama'a.
A yayin da ya ke magana bayan bayyana sakamakon, mataimakin shugaban karamar hukumar Sabon Gari, Abdulkareem Kamilu, ya bayyana jin dadinsa da irin halayyar da mambobin suka nuna a yayin da kuma bayan zaben.
Ya taya murna ga wadanda suka yi nasara da wadanda ba su yi nasara ba bisa irin halayya mai kyau da suka nuna wadda itace sanadiyyar kasancewar zaben wanda bai samu wata matsala.
A jawabinsa na amincewa, zababben shugaban, Alhaji Ahmadu Aboye, ya yi godiya ga Allah domin ba shi ikon jagorantar kungiyar wanda aiki ne da ya ke neman taimakon Allah.
Alhaji Aboye ya mika hannun 'yan uwantaka ga duk wadanda ba su yi nasara ba a zaben da su zo a hada kai domin cigaban kungiyar ta masu kasuwancin Timba.
Ya yi roko ga sauran mambobi da su ba shi cikakken goyon baya ta hanyar addu'o'i domin ya yi iya kokarinsa.
A cikin jawabinsa na bayar da shawara, mamba a cikin kungiyar Alhaji Alwa'u Bunkure ya nemi zababbun shugabannin da su ji tsoron Allah a cikin ayyukansu.
Alwa'u ya ma nemi mambobin da su taimaka masu da shawarwari masu kyau da addu'o'i.
0 Comments