Honorabul Aminu Yunusa ya zama Mainan Marmara
Daga Fatima Idris Zariya
A ranar Asabar 1/2/25 ne mai girmar sarkin Marmara Alhaji Musa Adamu ya naÉ—a Honorabul Aminu Yunusa a matsayin Mainan Marmara dake karamar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna.
Taron an gudanar da shine a ƙofar fadar Sarkin na Marmara dake Sabon Gari.
Daga cikin su akwai zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari kuma shugan kungiyar ciyamomin jihar Kaduna (ALGON) Chiarman Honorabul Abubakar Jamilu Albani Samaru da Honorabul Datti Muhammad Babawo da Ambasada suke Buba.dukkansu sun shaida naɗins Honorabul Aminu Yunusa a matsayin Mainan Marmara.
Hajiya Maimuna itace mahaifiyar shi Mainan Marmaran a zantawarta da manema labarai tayi fatan Allah ya sanyawa wannan matsayi da ÆŠanta ya samu kuma tayi ad'du'ar Allah ya sakawa Sarkin Marmara da alheri da ya baiwa Aminu Yunusa wannan matsayi.
Haka zalika babban yayansa Hajiya Fatima itama ta yi fatan alheri da wannan karamci da ƙaninta ya samu.
Hajiya Zakiyya Aminu Yunusa na daga cikin matansa itama tayi fatan Alheri ga samun wannan matsayi na Mainan Marmara da mai gidansu ya samu tace Allah ya taya shi riko kuma tayi addu'ar Allah ya maida kowa gidansa lafiya.
Daga karshen taron Mainan Marmaran yayi jawabin godiya ga dukkan wanda suka zo yashi murna kuma yayi jinjina ga mai martaba sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli da majalisar masarautar Zazzau da Hakimai da dukkan mutane ƙaramar hukumar Sabon Gari da jami'ar anguwa Marmara baki ɗaya.
Mawaƙa da masu wasan ƙwaikwayo da kungiyoyine suka gudanar da wasanni ciki har da Malam gundura da abokinsa sankace.
Anyi taro lafiya an tashi lafiya.
0 Comments