*Matasan Harkar Muslunci na yankin Katsina sun bada gudummawar jini (Blood Donation)*
Da safiyar Yau Laraba 29 Rajab,1446 dai-dai da 29/01/2025 Matasan Harkar muslunci na garin Katsina sun bayar da jini duk a cikin taya Al'umma murna da samuwar Maulana Amirul -Muminin Ali Bn Abu-Dhalib (As) wanda wakilan NBSC Katsina suka dauka a markazin Yan uwa dake kofar Marusa Katsina.
Bayan tashi daga karatun Ajin Laraba da Sheikh Yaqub Yahya Katsina yake gabatar ma da matasa,Wakilan na NBSC sun shiga sun gaisa da su Malam sannan suka yi masa ta'aziyyar rasuwar Malama Fatima Abdullahi (Uwar gidansa).
Acikin jawabin nasa Sheikh Yaqub Yahya Katsina yace" Binciken lafia lokaci bayan lokaci yana daga cikin Sharuddan gwagwarmaya dogaro da Hadisin Manzon Rahma (Saw) da yake cewa"Mumini kakkarfa yace muminin mai rauni."
0 Comments