Madrasatul Hidayatus Subyan Ila Ɗarikal jinan Bomo tayi bukin saukar ƙur'ani karo na 20
Daga Fatima Idris,Zariya
A cikin satin daya gabatadane makarantar Madasatul Hidayatul Subyan Ila Darikal Jinan Bomo ta zawiyar sheikh Yakub salihu Bomo mai Helƙwata, a garin Bomo dake ƙaramar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.
Yayin gudanar da bukin karo na 20 sarakuna da limamai da iyayen yara su halacci bukin tare da sanyawa bukin albaraka.
Sarkin Bomo Alhaji Muktar Salisu yayi jijina ka malamai da Ɗalubai da iyayen yara bisa ƙokarin da suka nuna da har aka sami nasarar kaiwa ga hakan.
Bayan kammala taro hakimin ƙasar Basawa Akitek Abubakar Haruna, Bamalli shima yayi jawabi tare da kira da a rungumi neman Ilmi don samun ci gaba rayuwa duniya da lahira.
Karshe hakimin yayi godiya ga al'umar kasar tasa bisa yadda suka rungumi zaman lafiya da mutunta juna kuma ya sanyawa Daluban da malaman albarkabisa namijin kokarinsu.
Bayan karbar shahadar ga dukkan Daluban an Karama wasu muhimman mutane bisa gudummawar da suke baiwa addinin Islama da ita kanta makarantar .don koyan addinin Allah.
Daga cikin wanda aka karrama aƙwai Honrabul Garba Datti Babawo da kuma zuriyar Shiek Yakubu Salis Bomo da sauran mutane masu yawa.
Anyi taro lafiya an tashi lafiya.
0 Comments