Kungiyar Rajin Cicciba Matasa Da Mata Ta Ziyarci Sheikh Zakzaky
Wata ƙungiya mai suna National Youths and Women's Support Initiative, mai rajin cicciɓa matasa da mata ta ziyarci Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), inda ta karrama shi da lambar girma a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da suka yi fice wajen ayyukan taimakon al'umma da kuma ci gaban ilimin mata a ƙasar nan. A gidansa dake Abuja.
A yayin da Jagora (H) ke yi wa tawagar jawabi, ya hore su da su kasance jakadun kawo haɗin kai da adalci da ci gaban al'umma. Ya kuma hore da su tsarkake niyyarsu, da ayyukansu. Jagora ya koka yadda ayyukan assha suka yawaita a cikin al'umma, musamman ma matasa da suke aikata laifuka kasar ta'ammuli da miyagun kwayoyi da sauran laifuka.
A yayin nashi jawabin shugaban tawagar, ya bayyana dalilinsu na miƙawa Jagora lambar girman, inda ya ce sun yi nazarin irin ayyukan da Jagora yake gudanarwa na taimakon al'umma, da maida hankali kan ci gaban ilimin mata da matasa. Kuma sun yi amfani da wannan damar don neman shawarwari don inganta ayyukan da suke gudanarwa.
0 Comments