Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Shaikh Zakzaky Ya Jajantawa Iyalan Waɗanda Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Turmitsitsi A Ibadan, Abuja Da Anambra


Shaikh Zakzaky Ya Jajantawa Iyalan Waɗanda Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Turmitsitsi A Ibadan, Abuja Da Anambra 

Daga Ammar M. Rajab 

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalai da ƴan uwan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin da ya auku a wajen bukukuwan Kirsimeti a Abuja, Ibadan, da Anambra.

A cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishinsa, Shaikh Zakzaky ya bayyana matuƙar alhininsa game da wannan mummunan lamari da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, "Jagora, Shaikh Ibraheem Zakzaky, yana miƙa ta'aziyya ga iyalai, 'yan uwa, da abokan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan Ibtila'in, tare da addu'ar Allah ya bai wa waɗanda suka jikkata lafiya."

Turmutsitsin, wanda ya faru a wurin rabin abinci domin bikin Kirsimeti, ya jawo hankulan al'umma tare da yin kira da a inganta tsare-tsare da matakan tsaro a yayin duk wani taron al'umma.

Haka nan saƙon Shaikh Zakzaky ya nuna matuƙar damuwarsa ga rayuwar ɗan Adam, kamar yadda ya jaddada a cikin addu’o’in da ya yi wa waɗanda suka jikkata da kuma ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu.

Post a Comment

0 Comments