Header Ads Widget

Responsive Advertisement

A taimaki Maimuna da jaririnta don girman Allah


A taimaki Maimuna da jaririnta don girman Allah

Daga Umar Idris,Zariya

Wani abin ban tausayi da sanya kuka ga duk mai imani a cikin zuciyarsa na aukuwa akan wani jariri da mahaifiyarsa a kwangila Zariya.

A safiyar yau Wakilinsu yaci karo da wata matashiya mai fama da matsalar taɓin hankali a wata anguwa da ake kira ƙwangila filai'oba Zariya dake karamar hukumar sabon Gari a jihar Kaduna.

Abin tausayin shine ganin halin da wata matashiyar budurwa ta shiga tare da jinjirin da ta haifa ƙanana 7 da suku gabata.

Kamar yadda kuke ganinta a hoto tare da jinjirinta da ta haifa a hannunta to bincike ya nuna cewa yau kwananta 7 da haihuwa kuma tana fama da ta'ɓin hankali kuma yanzu haka danginta basusan inda take ba gata ta fito da wan nan ɗanyen goyo.

Daga cikin abin tausayin shine yadda jaririn ke kwana a hunturun sanyi irin na Zariza babu mai taimakamasu sai Allah amma tana rungume da ɗan ta bata bari kowa ya taɓa shi.

Abu na biyu shine a matsayin ta na mai jego ya dace ace tana gasa mijinta da ruwan zafi akai akai to hakan bai samuwa ga wannan baiwar Allah sai dai wari dake tashi a mijinta Ya Allah ka tausaya mata.

Bisa wacan wari dake tashi a mijinta yasa mutane na ƙyamar zuwa kusa da ita ga jaririn mai lafiya amma ba mai taimakon gare su.

Bisa wannan hali da wannan baiwar Allah ta ke ciki walilinmu yayi ta maza yaje ya zanta da ita kamar haka.

Baiwar Allah tace sunanta Maimuna kuma sunan garinsu (mai Garaya) dake shiyar Kontagora a jihar Naija
Tace sunan mijinta Yakubu kuma Babanta shine tsohon mai anguwan garinsu ( mai Garaya )

Bisa haka muna kira ga al'umma da cewa a yaɗa wannan rahoto ko za a sami inda iyalan wannan baiwar Allah suke don da ita da jaririn nata da ta haifa ƙwana 7 da suka wuce suna cikin wani hali na tausayi kuma zaman tana laɓewa a lungunan yankin kwangila Zariya.

Post a Comment

0 Comments