Header Ads Widget

Responsive Advertisement

ZAƁEN NUJ TA ƘASA: Kwamitin tantance ƴan takara ya amince da takarar gogaggen ɗan jarida Garba Muhammad da wasu mutum biyu

ZAƁEN NUJ TA ƘASA: Kwamitin tantance ƴan takara ya amince da takarar gogaggen ɗan jarida Garba Muhammad da wasu mutum biyu

Muhammad Garba, editan jaridar News Express na yankin Arewacin Najeriya ya ya shiga sahun masu takarar shugabancin Ƙungiyar ƴan Jarida ta Ƙasa (NUJ).

Kwamitin tantancewar ya amince da takarar Muhammad tare da wasu mutane biyu, Al-Hassan Abdullahi Yahya daga kafar yaɗa labarai ta jihar Gombe (GMCTv), da Dele Atunbi na gidan talabijin ɗin gwamnatin tarayya (NTA) Abuja.

A ranar 26 zuwa 28 ga watan Nuwamba ne ake sa ran mutanen ukun za su kara da juna a yayin gangamin taron da za a yi a Owerri ta jihar Imo. Kuma duk wanda ya yi nasara a cikinsu shi ne zai maye gurbin shugaba mai barin gado, Chief Chris Isiguzoro, wanda ke kammala wa’adinsa na biyu.

Muhammad Garba gogaggen ɗan jarida ne da ya shafe sama da shekaru 30 yana aiki a gidajen jaridu da dama a ƙasar nan. Kuma jagora a tafiyar ƙungiyar ‘yan jarida wanda ke rajin kare haƙƙin mussaman ƴan jarida.

Ɗaya daga cikin manufofin Garba shi ne inganta walwalar ‘yan jarida a faɗin ƙasar nan kuma da ma mutum ne da ya yi fice a wannan ɓangare.

Wani abun alfahari game da takararsa shi ne zama ɗan jarida mai zaman kansa a tsakanin abokan karawarsa. Wannan a cewar magoya bayansa ya isa ya ba shi ƙarfin guiwar ƙwato wa ‘yan jarida haƙƙoƙinsu ba tare da fargaba ba.

Ƙungiyar ‘yan jarida dai ƙungiya ce wacce ke da rassa a jihohin Najeriya da kuma ke ƙoƙarin kare haƙƙin ‘yan jarida da aikinsu.

Post a Comment

0 Comments