Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Bamu yarda da dauke Tashar Daɗi motors Park ba zuwa Yan Ƙarfe -- Inji kungiyoyin Sufuri

Bamu yarda da dauke Tashar Daɗi motors Park ba zuwa Yan Ƙarfe -- Inji kungiyoyin Sufuri 

Daga Umar Idris, Zariya



Kungiyoyin sufuri sun gudanar da jerin gwano a anguwar ƙwangi dake ƙaramar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Kungiyoyin sun haɗa da NURTW da NATO da RTEAN reshen karamar hukumar ta Sabon Gari Zariya.

Yayin gudanar da zanga-zanga kungiyoyin sun ɗaga kwalaye mai dauke da nuna koke zuwa ga sabon shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari Honorable Abubakar Jamil Albani Samaru da ya tausaya masu akan bakar azabar da suke ciki na ɗauke tashar motar ( Daɗi- Motors Park) zuwa Yan ƙarfe da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari yayi Honorabul Injiniya Ibrahim Usman yayi yayin da yake karagar mulkin sa .

Shugabannin kungiyoyin uku tare da rakiyar lauyoyinsu ne suka jagoranci jerin gwanon har zuwa ofishin shugaban karamar hukumar Honorabul Abubakar Jamil Albani Samaru.

Barista A U Haji shi ya mikawa shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari takardar koken nasu tare da sanar dashi halin da al'ummar dake gudanar da harkoki a gurin suke ciki.

Lauyan yace hanyoyin da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari Honorable injiniya Ibrahim Usman yabi na ɗauke tashar Daɗi motors Park daga Kwangila zuwa Yan Ƙarfe bai bi dokar ƙasaba don haka jama'ar da yake karewa suna son ayi masu adalci a dawo da tashar inda take a lokacin baya.

Bayan Shugaban ƙaramar hukumar Honorabul Abubakar Jamil Albani ya saurari ƙorafin gamayyar kungiyoyin tare da karbar takardan koken daga Lauyansu ya janyo hankalin gamayyar kungiyoyin cewa lailai ya yaba da matakan da suka dauka na hankali.

Honorabul Albani ya ƙara da cewa zai gudanar da bincike akan lamarin don daukar matakin da ya dace game da lamarin.

Ƙarshe yayi godiya ta musamman ga gamayyar kungiyoyin bisa yadda suka girmamashi basuyi wani tashin hankali ba yayin gabatar da koken nasu.

Wakiliyarmu ta zanta da shugaban NURTW reshen karamar hukumar Sabon Gari Malam Abubakar Sadik, game da lamarin kuma yayi masa ƙarin haske akai yace, 

Da farko yace, mayar da Dadi Motors Park Yan Ƙarfe baiyi Tsariba saboda mafi akasarin direbobi ba sa shiga ciki, saboda Fasinjoji ba su gamsu da zuwa wurin ba, saboda dalilai kamar haka.

Na biyu wurin bai yi center ba, kamar yadda dadi Motor park take center na zuwa ko ina, kuma daga ko ina.

Na Uku akwai barazanar tsaro a wurin ta yadda in dare yayi Yan Kasuwa, Fasinjoji da Ma'aikata na cikin fargaba da razani.

Na huɗu akwai tsoron ababaen hawan da ke Kai komo a highway wanda komai na iya faruwa.

Na biyar kudin motan ya karu, kuma Fasinjoji basu da isassun kudin da za su hau Mashin, ko Keke Napep su je wurin. Ga Karin kudin mota fiye da yadda su ke hawa a Dadi Motor park.

Bugu da ƙari abin da Karamar Hukumar Sabon Gari ke samu na Revenue a Tashar Dadi Motor park. Ba ta samun kaso Arba'in a yanzu, saboda dalilai kamar haka;

Kuma yanzu haka babu Motocin da ke shiga Lodi sosai, kuma ko sun shiga sai dai su yi zaman jira, saboda ba Fasinjoji.

A yanzu haka harkar kasuwanci ba ya tafiya a wurin kamar yadda ya ke tafiya a Dadi Motor park, saboda Al'umma sun kauracewa wurin.

Yanzu haka a maimakon revenue da ya ke shiga Asusun Karamar Hukumar Sabon Gari yanzu ya koma shiga na Karamar Hukumar Zaria inda kusan lodin ya koma Dan Magaji da Agwaro. Sai Kuma Karamar Hukumar Kudan.

A yanzu haka mutane da dama sun ajiye aikin tashar; Wasu Kuma sun ajiye Motocin sai Yan Kasuwar da su Ka yi hijira, saboda tsananin rashi da ke yawo a Tashar. To, dawo da ita inda ya ke Shi zai dawo da martabar harkar sufuri a Karamar Hukumar Sabon Gari, kuma Matan da aka saka saboda tashin tashar ana iya dawo da su. 

Ya kamata a lura da cewa martaba, kima da daraja na Jam'iyyar APC zai iya dawowa, saboda Babban bakin jinin da ta yi bayan kuncin rayuwa da Mutane ke ciki shine tashin tashar da ya dada masu Lodi. Mabanbantan Mutane ne a wurin tun daga Karamar Hukumar Sabon Gari da Zaria ba ana maganar Yan Kwangila ba ne da su Ka kasance 5%.

Adawo da dadi moto park inda take zai kara haɗa kan al'ummar karamar hukumar Sabon da ikon Allah.
tun da aka ɗauke tashar Daɗi motors zuwa Yan Ƙarfe mutane Arewa matafiya ke fuskanta kalubalen kala-kala.

Malam Abubakar ya kara da cewa bisa haka ne yasa suka haɗa kai suke neman sabon shugaban ƙaramar hukumar Sabon Honorabul Abubakar Jamil Albani Samaru bisa adalcin sa ya dawo da tashar inda take a lokacin baya.

Malam Baba, K shine shugaban kungiyar sufuri na RTEAN reshen karamar hukumar Sabon Gari shima ya tabbatar da cewa mutanen da suke cin abinci karkashin Dadi Motors Park suna da yawa amma yanzu ɗauketa a Kwangila zuwa Yan Ƙarfe ya haifar da matsalolin masu yawa ta bangaren tsaro da kiyaye lafiyar matafiya.
Don haka yayi kira ga sabon shugaban makarantar hukuma ya taimaka ya dawo da tashar inda take a lokacin baya.

Malam Habibu shine ya jagorancin kungiyar sifiri ta NATO reshen karamar hukumar ta Sabon Gari a wannan waje shima ya nuna ɓacin ransa sosai kuma yayi kira da gaggawa cewa a ceto rayuwar matafiya daga halin da suke ciki na rashin kwanciyar hankali da suke fama dashi na matsalar dawo da tashar motar Daɗi- Motors zuwa Yan Ƙarfe yace gaskiya babu alheri domin gurin bai dace da tashar motaba.

Honorabul Jibirin Sani Sambo shine zaɓabben kasilar Hanwa a yanzu haka shima ya tabbatar da goyon bayan kungiyoyi tare da kira ga shugaban makarantar hukumar Sabon Gari daya taimaka ya dawo da tashar inda take a lokacin baya.

Kungiyoyin sun gudanar da gangamin lafiya sun gama lafiya.

Post a Comment

0 Comments