Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Shin akwai daɗi mai illa da muke amfani dashi a matsayin abincinmu

Lafiya Uwar jiki

Daga Idris Umar, Zariya

Tsaraba daga abokan zumunci na yanar gizo akan lafiyar mu.

Shin akwai daɗi mai illa da muke amfani dashi a matsayin abincinmu?

Daɗin dake naƙasa mutane a hankali a Hankali

Nama (Meat) na daga cikin kayan daɗi da mutane ke jin daɗin mu'amala dashi. Sannan mutane na kashe kuɗi sosai wajen siyan shi.

Abinda mutane da yawa basu sani ba ne, Nama iri-iri ne, akwai wanda yawan cin shi na haifar da barazana ga lafiyar ɗan Adam. Misalin irin wannan naman mai iya haifar da matsaloli shi ne JAN NAMA/NAMAN/SANIYA/SHANU (BEEF) da kuma NAMAN DA AKA SARRAFA SHI DA INJI (PROCESSED MEAT).

Duk da cewa shi naman SANIYA (BEEF) yana da amfani a jiki ta hanyar bada Sinadarai masu muhimmanci, yawan cin shi na haifar da wasu matsaloli masu matuƙar barazana ga lafiya.

Ga matsalolin da yawan cin JAN NAMA (BEEF) ke haifar wa:

1. JAN NAMA na ɗauke da matsatstsen kitse da kwalastarol (saturated fats and cholesterol) mai yawa a cikin shi. Kayan abinci masu ɗauke da wannan abubuwan suna ƙara yawan su a jiki wanda hakan na iya haifar da matsala ga lafiyar Zuciyar Mutum.

2.  Yawan cin JAN NAMA na iya haifar da matsaloli ga lafiyar cikin mutum, musamman kumburin ciki.

3. Yawan cin JAN NAMA na iya haifar da CIWON DAJI NA HANJI+DUBURA (COLORECTAL CANCER), wannan lamari ne da bincike (researches) da yawa sun tabbatar.

4. Yawan cin JAN NAMA na iya haifar da matsalar ciwon ƙafa, sanyin kashi (Arthritis) da ƙaruwar sinadarin URIC ACID a jiki.

5. Yawan cin JAN NAMA na taimakawa wajen haifar da cutar ƙiba (Obesity).

Ba gwaninta bane mutum ya zauna yayi ta cin naman da yawa a zama ɗaya, balle JAN NAMA. In za'a ci a ci daidai wa daida.

Cin naman kaza, na akuya da kifi sun fi lafiya akan na saniya, su ma ɗin ya kasance daidai gwargwado.

Allah ya ƙara mana lafiya

Copy....

Post a Comment

0 Comments