Header Ads Widget

Responsive Advertisement

KIWON LAFIYA: Gwamnan Zamfara Ya Jinjina Wa Takwaransa Na Jihar Edo



Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba wa Gwamna Godwin Obaseki kan yadda ya kawo sauyi da kuma ƙudirinsa na inganta fannin kiwon lafiya na Jihar Edo.

Gwamnan ya kasance babban baƙo a wajen bikin ƙaddamarwa, rantsar da sababbin ɗalibai da kuma cika shekaru 60 da kafa Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da Fasaha ta Edo (EdoCOHEST) da aka gudanar a birnin Benin a ranar Larabar da ta gabata.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa bayan ƙaddamar da kwalejin, gwamnonin sun zagaya da kayayyakin zamani da aka samar a ginin.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Lawal ya ba da shawarar cewa jihohin biyu su kafa shirin musayar É—alibai, wanda zai bai wa É—alibai mata da ke makarantun kiwon lafiya a Zamfara damar zuwa kwalejin Edo domin yin wani zagon karatu.

Ya ce, “HaĆ™iĆ™a babban abin alfahari ne da kuma gata kasancewata a nan wurin tare da É—an uwana da mutanen kirki na jihar Edo don buÉ—e wani sabon babi na Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiyar da Fasaha ta Edo, musamman ga É—aliban da suka shigo yanzu.

“Yayin da muka taru a nan, ina jinjina irin hangen nesa da jajircewar É—an uwana Gwamna Obaseki, wanda ya sake farfaÉ—o da fata a Jihar Edo cikin kyakkyawar manufa, za a iya samun É—aukaka duk da rashin daidaito a Ć™asarmu mai albarka.

“Lokacin da na samu bayanai game da wannan ingantaccen aikin gaba É—aya, na yaba kuma na jinjina wa É—an uwana kan irin wannan manufa da za a iya cimmawa kaÉ—ai ta bangaren juriya, hangen nesa da sadaukarwa.

“Ga É—aliban da suka shigo a yau, zan ce ku ne burinmu kuma alfaharinmu. Kuna wakiltar jihar Edo da Ć™asar mu gaba É—aya ne. Don haka kada ku iyakance kanka.

“Ku yi karatu kuma ku yi fice a karatun; ku daraja aikin da É—an uwana ya yi a yau don kanku da É—alibai a nan gaba.

“Baya ga samar da Ć™wararrun masana kiwon lafiya, ina addu’a cewa wannan kwaleji ta zama wata gada ta haÉ—a kan jama’a, samar da ayyukan yi, da bunĆ™asar tattalin arziki a ciki da wajen jihar Edo. ”

Gwamna Obaseki ya gode wa Gwamna Lawal bisa girmama gayyatar da mutanen jihar Edo suka yi masa

“Ina matuĆ™ar godiya da kai É—an uwana Gwamnan Jihar Zamfara, Dokta Dauda Lawal da ka zo min wannan biki mai bangarori uku, wanda ya hada da Ć™addamarwa, rantsar da sabbin É—alibai, da kuma  cika shekaru 60 da kafa Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da Fasaha ta Edo (EdoCOHEST)."

Post a Comment

0 Comments