KASUPDA ta rushe gidan wani injiniya a Kaduna
Daga Idris Umar, Zariya
A ranar Lahadin da ta gabata ne Hukumar Raya Birane ta jihar Kaduna (KASUPDA), ƙarƙashin Gwamnatin Jihar Kaduna ta rusa wani gida mai shekaru 22 mallakin Injiniya Yahya Gilima, wani fitaccen Injiniyan gine-gine a jihar.
Wannan gida da aka rusa kammalallen gida ne da ke lamba 11, Titin Yahya Imam da ke Malali a Kaduna, wanda Injiniya Gilima ya mallaka tun a shekarar 2002, inda aka fara aikin ginawa nan take, sannan aka kammala a shekarar 2003.
Sai dai kuma a ranar Juma’a, kwatsam sai suka wayi gari an liÆ™a masu wata sanarwa a jikin bangon gidan, inda ake neman da su kwashe duka kaya gidan cikin sa’o’i 48 ko kuma a rushe tare da su.
A wani taron manema labarai da ya gabatar a harabar gidan a Kaduna, Injiniya Gilima ya bayyana mamaki da takaicinsa kan lamarin, inda ya ce an kawo masa sanarwar ne a ranar Juma’a, ranar da ba a zuwa aiki a jihar Kaduna, wanda hakan ya sa ya kasa bayar da amsa nan take.
“Ina jiran ranar Litinin ne ta yi in gabatar da Æ™orafina ga sanarwar da KASUPDA ta liÆ™a a jikin gida, amma sai suka zo da misalin Æ™arfe 11 na dare tare da jami’an tsaro a cikin shirin yaÆ™i, suka kore mu daga gidan, suka fara rusawa” inji shi.
Lamarin dai ya jawo cece-kuce a jihar, inda da dama ke kallon hakan a matsayin take ’yancin Injiniya Gilima a matsayinsa na É—an Nijeriya na mallakar fili ko gida ba tare da tsangwama ko tsoratarwa ba. An nuna damuwa game da ayyukan gwamnati da ‘yancin ‘yan Æ™asa.
Injiya Gilima ya ci gaba da bayyana cewa, shi dai abin da ya sani shi ne sun kwashe kimanin shekaru tara suna shari’a da wani mutum wanda ya taÉ“a aiko masa cewa wai filin sa ne, wanda kuma yanzu haka maganar tana kotu.
“Saboda haka ni na yi mamakin ganin yadda gwamnatin ta É—auki wannan mataki alhali maganar na gaban Æ™uliya.
0 Comments